Vladimir Putin (Russian: Владимир Путин) shine shugaban ƙasar Rasha na yanzu. An haifi Putin ne a Leningrad, indaa a yanzu ake kira Saint Petersburg, a ranar 7 ga Oktoba 1952. Ya kasance Firayim Ministan Rasha daga 1999 zuwa 2000, sannan Shugaban Rasha daga Maris 2000 zuwa Mayu 2008, kuma Firayim Minista kuma daga 2008 zuwa 2012. Ya zama shugaban kasa. Kuma a cikin 2012. Tun da farko ya sami horo a matsayin lauya.[1][2]
An haifi Putin ne a ranar 7 ga Oktoba 1952, a Leningrad, Taraiyar Sobiyat (yanzu Saint Petersburg Russia). Iyayensa su ne Vladimir Spiridonovich Putin (1911-1999) da Maria Ivanovna Putina (née Shelomova; 1911–1998). Spiridon Putin, kakan Vladimir Putin, ya kasance mai dafawa Vladimir Lenin da Joseph Stalin.[3][4]
Daga 1985 zuwa 1990, Putin ya yi aiki da KGB, sabis ɗin leƙen asiri na Tarayyar Sobiyat. Putin ya yi aiki a Dresden, wanda wani yanki ne na tsohuwar Jamus ta Gabas. Bayan Jamus ta Gabas ta ruguje a 1989, an gaya wa Putin ya dawo Tarayyar Soviet. Ya zaɓi ya tafi Leningrad, inda ya tafi jami'a. A cikin watan Yuni 1990, ya fara aiki a sashen harkokin kasa da kasa na Jami'ar Jihar Leningrad. A watan Yuni 1991, an nada shi shugaban kwamitin kasa da kasa na ofishin magajin garin Saint Petersburg. Aikinsa shi ne inganta dangantakar kasa da kasa da zuba jari a kasashen waje.[source?]
Putin ya bar muƙaminsa a KGB a ranar 20 ga Agusta, 1991, lokacin da ake gwabzawa da Shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev. A 1994, ya zama na farko mataimakin shugaban birnin Saint Petersburg. A watan Agustan 1996, ya zo Moscow, kuma ya yi aiki a manyan mukamai daban-daban a gwamnatin Boris Yeltsin. Ya zama shugaban FSB (sabis na leƙen asiri a cikin Rasha ɗan jari hujja na zamani) daga Yuli 1998 zuwa Agusta 1999, kuma ya kasance Sakataren Kwamitin Tsaro daga Maris zuwa Agusta 1999.
Putin ya zama Shugaban Rasha a watan mayu 2000. Putin shi ne shugaban jam'iyyar United Rasha mai mulki. Tun bayan faɗuwar Tarayyar Soviet ne dai wannan jam'iyyar ke lashe zaben kasar Rasha.
Masu sukar Putin sun ce ya ƙwace ƴancin jama’a, kuma ya kasa inganta ƙasar. Rasha tana samun kuɗi da yawa daga sayar da mai da iskar gas zuwa wasu ƙasashe, amma saboda cin hanci da rashawa, ba a amfani da wannan kuɗin don inganta yanayin rayuwa.[5][6]
A baya-bayan nan dai ƴan adawar Rasha sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Putin, inda suka yi kamfen na nuna adawa da Putin ta yanar gizo, tare da buga rahotanni masu zaman kansu ga sauran jama'a. Saboda sa baki a cikin kafofin watsa labarai, yana da matukar wahala a sami bayanai daban-daban ga jama'a.
Putin ya yi adawa da mamaye Libya a shekarar 2011. Yana kuma adawa da mamaye Syria da Iran.
A ranar 24 ga Maris, 2014, an dakatar da Putin da Rasha daga G8