[go: up one dir, main page]

Jump to content

Theophilus Yakubu Danjuma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Theophilus Yakubu Danjuma
Ministan Tsaron Najeriya

ga Yuni, 1999 - Mayu 2003 - Rabiu Kwankwaso
Aliyu Muhammad Gusau

ga Yuli, 1975 - ga Afirilu, 1980
David Ejoor - Ipoola Alani Akinrinade
Rayuwa
Haihuwa Takum, 9 Disamba 1938 (85 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Daisy Danjuma
Grace Danjuma (en) Fassara
Yara
Karatu
Makaranta Jami'ar Tsaron Nijeriya
Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa da ɗan siyasa

Theophilus Yakubu Danjuma anfi sanin sa da T. Y. Danjuma (an haifeshi ranar 9 ga watan Disamban shekarar 1938) a garin Takun ta tsohuwar jahar Gwangola wacce a yanzu ƙaramar hukuma ce a cikin jahar Taraba. Sunan mahaifinsa Kuru Ɗanjuma, mahaifiyarsa kuma sunanta Rufƙatu Asibi. Shi ɗan ƙabilar Jukun ne.[1]

Janaral Theophilus Ɗanjuma, ya yi karatunsa na firamare da sikandire a makarantun ‘St Bartholomew's Primary School’ da ke Wusasa ta Zariya , da kuma ‘Benue Provincial Secondary School’ da ke Katsina-Ala ta cikin jahar Binuwai. Inda ya kammala a shekarar 1958. Daga nan Theophilus Ɗanjuma ya samu nasarar shiga makarantar ‘Nigerian College of Arts Science and Technology’ ta Zariya wacce yanzu ta koma jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (Ahmadu Bello University) a shekarar 1959, dan karantar fannin tarihi (History), sai dai, ya bar wannan makaranta a shekarar 1960 ya koma makarantar sojojin Najeria (Nigerian Military Training College) ta Kaduna, inda ya yi karatu daga shekarar 1960 zuwa 1961. [2]

Theophilus Yakubu Danjuma

Sannan kuma ya samu halartar ‘Mons Officer Cadet School’, da ke garin Aldershot, a ƙasar Birtaniya (United Kingdom). Sannan ya yi karatu a ‘School of Infantry’, da ke garin Hythe da Warminster a shekarar 1962, sai kuma ‘Special Warfare Centre’ a shekarar 1963, da kuma ‘Army Staff College’ a shekarar 1967, duk a ƙasar Birtaniya (United Kingdom).

Gogayyar Aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Tun bayan kammala samun horansa na soja, Janaral TY Ɗanjuma mai ritaya, ya riƙe muƙamai da dama, daga ciki akwai: 1. An fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). A shekarar 1963, an tura shi rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya ta samar da zaman lafiya (UN Peace-keeping force) a garin Sante, da ke lardin Kataga a ƙasar Kwango (Congo). 2. A shekarar 1966 aka ƙara masa girma zuwa Kyaptin (captain) ɗin soja. A shekarar 1967 aka sake ɗaga shi zuwa laftanar kanal (lieutenant Colonel). 3. A shekarar 1970, TY Ɗanjuma ya wakilci Najeriya a ‘International Court Martial in Trinidad and Tobago’ a matsayin ‘president of the tribunal’ inda ya jagoranci kotun da ta tuhim yunƙurin juyin mulkin da aka yi a Trinidad da kuma Tobago. 4. 1971 aka ɗaukaka shi zuwa kanal (Colonel) da kuma muƙamin ‘court-martialling Army officers’ da ya jagoranci kula da yaƙi da rashawa da kuma ɗa’ar sojoji. 5. A 1975, ya zama birgediya (brigadier) wanda aka yi masa muƙamin ‘General Officer Commanding (GOC)’. A 1976 aka yi masa muƙamin shugaban rundunar sojojin ƙasa na Najeriya (Chief of Army Staff) a lokacin mulkin shugaba Ubasanjo a matsayin soja. 6. ‘Chairman of the Presidential policy Advisory Committee’, 1999. 7. ‘Honourable Minister of Defence’, 1999 zuwa 2003. 8. ‘Chairman of the Presidential Advisory Council’, tun daga 2010 har zuwa yau (2016). [3]

9. Shugaban kwamtin sake tsungunar da ‘yan gudun hijirar Najeriya (Internally Displaced Persons), muƙamin da shugaba Muhammadu Buhari ya ɗana shi a shekarar (2016). Kasuwanci A shekarar 1979, ya buɗe kamfanin fito (Shiffing) mai suna America Line (NAL), kamfanin da ya samar da guraben ayyuka na sama da mutane 251. Shi ne mai kamfanini COMET Shipping Agencies Nigeria Ltd., wanda aka buɗe shi a shekarar 1984. A shekarar 1995, T.Y. Ɗanjuma, ya shiga harkar mai inda ya buɗe kamfani mai suna South Atlantic Petroleum Limited (SAPETRO). [4]

Tun baya miƙa mulki ga hannun farar-hula, TY Ɗanjuma ya shiga siyasa, kuma tun wannan lokaci ake damawa da shi har zuwa yau ɗin nan (2021).

  1. "BOC Gases Changes Name After TY Danjuma's Acquisition of 72 Stake".
  2. https://military-history.fandom.com/wiki/Theophilus_Danjuma
  3. https://punchng.com/ty-danjumas-firm-buys-additional-60-stake-in-boc-gases/
  4. https://www.vanguardngr.com/2021/07/breaking-ty-danjuma-still-alive-family-debunks-death-rumours/