[go: up one dir, main page]

Jump to content

Tamale, Ghana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tamale, Ghana


Wuri
Map
 9°24′27″N 0°51′12″W / 9.4075°N 0.8533°W / 9.4075; -0.8533
Ƴantacciyar ƙasaGhana
Yankuna na GhanaYankin Arewaci
Gundumomin GhanaTamale Metropolitan District
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 466,723 (2016)
• Yawan mutane 622.3 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Harshen Dagbani
Labarin ƙasa
Yawan fili 750 km²
Altitude (en) Fassara 151 m
Sun raba iyaka da
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo tamale.ghanadistricts.gov.gh

Tamale birni ne mai saurin cigaba a Yammacin Afrika. Shine babban birnin arewacin kasar Ghana. Birnin cibiya ce ta kasuwanci a yankin. Waje ne mai kwanciyar hankali sannan kuma mai sauki wajen kasuwanci. Mutanen birnin mutane ne masu son zaman lafiya. Tamale shine birni na uku mafi girma a kasar Ghana. Yana da yawan jam'a kimanin 950,124 kamar yadda shafin yanar gizo mallakin birnin ya ruwaito. Shine birni mafi saurin cigaba a Yammacin Afrika.[1][2] Birnin na a 600 km (370 mi) north of Accra.[3]

Mafi akasarin mazauna birnin Tamale Musulmai ne, akwai Masallatai da dama a Tamale, mafiya shahara sune, Masallacin Afa Ajura (masallacin Ambariyyah), da kuma masallatan kungiyar da'awa ta Ahmadiyya.

Tamale na a Arewacin Ghana ne, asalinta daga masarautar Dagbon ta fita. Sarkin shine sarkin al'umar Dagomba wato sarkin Yendi.

Sakamakon kasantuwar Tamale a tsakiya ne yasa birnin yazama matatara ta gudanarwar gwamnati da cibiyar kasuwanci da siyasa a arewacin Ghana.[4]

Cigaban Tamale yazo ne cikin shekaru kadan da suka gabata .[5]

Ofishin magajin birnin Tamale

Tsarin Gwamnatin Tamale na tafiya ne karkashin ofishin magajin gari wanda shugaban kasar Ghana ne keda ikon nada shi. Magajin garin T Tamale na yanzu shine Hon. Iddrisu Musah. Akwai majalisa mai dauke da wakilai yan majalisu masu gudanarwa.

Sabuwar Jami'ar University for Development Studies (UDS)

Tamale nada muhimmancin gaske a fannin ilimi a kasar Ghana. Ya zuwa yanzu, akwai makarantu 742 a tsakiyar birnin. Wannan ya hada da makarantun Nazire guda 94, Firamare 304, kananan sakandare 112 da kuma manyan sakandare 14. Sauran sun hada da makarantu na koyo a aikace, sai kwalejin ilimi biyu, jami'ar fasaha da wasu jami'oi biyu masu zaman kansu.[5]


Makarantun Sakandire a tamale

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Tamale Senior High School
  • Ghana Senior High School (Tamale)
  • Northern School of Business
  • Business Senior High School
  • Tamale Girls Senior High School
  • Viting Senior High School
  • Kalpohin Senior High School
  • Tamale Islamic Science Senior High School
  • St Charles Senior High School
  • Adventist Senior High School
  • Presbyterian Senior High School
  • Business College International
  • Tamale Girls International School
  • Ambariya Senior High School
  • Dabokpa Technical and Vocational School
  • T- Poly Senior High School
  • Abubakar Al-sadiq Senior High School
Motar haya ta Bus a Tamale

Tamale nada muhimmancin gaske a fannin sufuri a kasar Ghana. Akwai Filin jirgin saman Tamale..[6]

Akwai motocin haya na tasi, da babura masu kafa uku wadanda ake kira da "Mahama-Cambuu". Su Mahama Cambuu sunane da aka lakabawa babura masu kafa uku ma'ana " Mahama zai yi". Mahama din shine tsohon shugaban kasar Ghana, H.E John Dramani Mahama. Suna da sauki ba kamar tasi ba, kuma zasu kaika dukan lungun da zaka. Akwai kuma babura masu kafa biyu wadanda akafi sani da yan acaba.

Hotunan wasu sassa daga birnin Tamale.

  1. GhanaWeb.com ghanaweb.com
  2. "The largest cities in Ghana, ranked by population". Mongabay.com. 2013. Retrieved 1 May 2014.
  3. Tamale, Northern Region (Ghana) Archived 2011-07-24 at the Wayback Machine. icli.nl.
  4. Tamale, capital of Northern region, Ghana. ghana-net.com.
  5. 5.0 5.1 Tamale Children's Home Tamale, Northern Region (Ghana) Archived 2011-07-25 at the Wayback Machine. catointl.org
  6. Tamale Airport Listings Archived 2012-03-02 at the Wayback Machine. Ghanapedia.