Mata a musulunchi
Mata a musulunchi | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | gender role (en) da female topic (en) |
Amfani | kyawawan aiki a musulunci, Nikah da Polygamy in Islam (en) |
Facet of (en) | women and religion (en) |
Significant person (en) | Khadija Yar Khuwailid, Fatima da Maryam a Musulunci |
Sana'a | bauta a musulunci, aiki a musulunci da Ilimi a Musulunci |
Addini | Musulunci da Sufiyya |
Bisa | women in the Qur'an (en) |
Ta jiki ma'amala da | Islam and children (en) , gender segregation and Islam (en) da childbirth in Islam (en) |
Alaƙanta da | Orientation of children in Islam (en) da parenting (en) |
Abu mai amfani | Islamic clothing (en) , Tasattur (en) da Hijab |
Kiyaye ta | God in Islam (en) |
Including (en) | ritual purity in Islam (en) , hayd (en) , Nifas (en) da Istihadha (en) |
Mata a musulunci Suna da matukar daraja da kima a musulunci. wannan ne ya sa har (Allah SWT) ya saukar da Surah guda acikin littafi mai tsarki AlQur'ani wacce ta yi bayani dangane da sha'anin mata wato ; SURATUN-NISAA'I ma'ana: surar da ke magana kan sha'anin mata.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin zuwan musulunchi mata sun kasance basu da wata kima a wajen mutane Kuma basu da wani 'yanci. Kafin zuwan musulunchi mutane suna kyamar mata matuka wannan ne yasa mutum baya son a haifar mishi jaririya mace idan an haifeta zai je ya haka rami ya binne ta da ranta. Kuma dai a wancen lokacin mata basu da wani hakki face yanda aka yi da su, basu da rabon gado saidai ma a gajesu Kamar wasu dawaki.
Da zuwan musulunchi mata suka Sami 'yanci suka zama 'yan gata ababan girmamawa ta yanda Allah ya dora nauyin kula da su daya hada da Ciyarwa,muhalli,Tufatarwa,kare lafiya, ilimantarwa, kyautatawa, da dai sauransu a kan mazaje. Musulunchi ya ba mata dukkan hakkin daya kamata a ba su hadi da kyautatawa ba tare da tozarta rayuwarsu ba. Musulunchi ya dora nauyin kula da mace a kan iyayenta lokacin da take karama, daga lokacin da ta girma ta yi aure to nauyin ya koma kan mijin daya aureta, da zaran Kuma ta tsufa to dole ne 'ya'yanta da mijinta su kula da rayuwarta. Musulunchi ya ba mata damar su gaji duniyar da iyayensu ko mazajensu suka mutu suka bari Kamar yanda addinin musulunchi ya tsara. Babu wani addini da ya girmama mata Kamar musulunchi domin kuwa shi ne addinin daya daukewa mata dukkan wahal-halun rayuwa na Neman abinci ko abinda Ya yi kama da haka, ya dora nauyin a kan maza su kuma mata aka ba su damar su zauna su huta Mike kafa a yi musu komai.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Ƴan mata sanye da hujabi
-
Wata sanye da Hijabi