[go: up one dir, main page]

Jump to content

Osinachi Ohale

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Osinachi Ohale
Rayuwa
Haihuwa Owerri, 21 Disamba 1991 (32 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Harshen, Ibo
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Rivers Angels F.C. (en) Fassara2008-2009
Delta Queens (en) Fassara2010-2014
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya2010-
Houston Dash (en) Fassara2014-2014191
Rivers Angels F.C. (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 173 cm

Osinachi Marvis Ohale (An haifeta a ranar ashirin da daya 21 ga watan Disamba a shekara ta alif 1991)[1] ta kasance yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta kasarvNijeriya, wacce take buga baya, kuma tana buga ma gasar Seria A ta mata, a ƙasar italiya ga kulob din A.S Roma, kuma tana cikin tawagar kwallon kafa ta mata a Najeriya.[2][3]

Kariyan ta na kulub

[gyara sashe | gyara masomin]

Ohale tana taka leda a Houston Dash a kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasa a duk tsawon shekarar dubu biyu da goma Sha hudu 2014 kafin ta dawo gida Najeriya tare da Rivers Angels .[4][5]

A shekarar dubu biyu da goma Sha shida 2016, ta shiga kungiyar kwallon kafa ta Sweden Damallsvenskan ta Vittsjö GIK, inda ta buga wa kungiyar wasa har sau 22 kafin ta koma Vaxjo DFF watanni goma sha takwas daga baya a cikin watan Agusta na shekara ta 2018.[6]

A ranar sha daya11 ga watan Satumbar a shekara ta( 2019) ta sanya hannu kan CD Tacón ta Sipaniya a kan canjin dindindin, ta buga wasanta na farko a kulob din a wasan da ta doke Sporting de Huelva da ci 3-0 kwanaki uku kacal.[7]

Osinachi Ohale

A ranar 30 ga watan Yulin a shekara ts (2020) ta rattaba hannu a kan kungiyar AS Roma ta mata, dan Najeriyar ya rabu da kungiyar CD Tacon ta kasar Sipaniya, wacce a yanzu ake wa lakabi da Real Madrid a watan da ya gabata (Yunin shekarar 2020) bayan karewar kwantiragin ta da kamfanin Primera Iberdrola . Ta shiga kungiyar mata ta Serie A din ne a kan yarjejeniyar shekara daya kan kudin da ba a bayyana ba. Dangane da matsayinta na tarihi, Ohale ta fada wa gidan yanar gizon kungiyar: [8] “Na zabi Roma ne saboda abubuwa da yawa; abubuwan ban mamaki da yawa game da kulob din, game da wannan birni da kuma wannan ƙasa da suka ba ni sha'awa. " "Na ji kamar zai zama babban abu a gare ni, bincika da kuma fuskantar sabbin abubuwa da sabon ƙalubale." [9]

Kariyanta na duniya

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta wakilci Nijeriya a wasannin Gasar Mata na Afirka na shekara ta 2010, da 2014, da 2016 dakuma 2018. Ta lashe gasar a duka lokuta hudun.

Osinachi Ohale cikin yan wasa

Ta kuma kasance a cikin 'yan wasan Najeriya na FIFA na Kofin Duniya na Mata a shekara ta 2011, da 2015 dakuma 2019[10]

Lamban girmaa

[gyara sashe | gyara masomin]
Delta Queens FC
  • Gasar Matan Nigeria (2): 2011, 2012
Najeriya
  • Kofin Kasashen Afirka na Mata (4): 2010, 2014, 2016, 2018

Kowane mutum

[gyara sashe | gyara masomin]
  • IFFHS CAF Matan Tawaga na[11]
  1. "List of Players – 2015 FIFA Women's World Cup" (PDF). Fédération Internationale de Football Association. Archived from the original (PDF) on 10 April 2016. Retrieved 20 June 2015.
  2. "Profile". FIFA.com. Archived from the original on 15 August 2018. Retrieved 20 June 2015.
  3. "Player profile". Houston Dash. Retrieved 29 June 2015.
  4. "Osinachi Ohale's route to United States, Houston Dash is an answer to prayers". Houston Dash. Houston Dash Website. Archived from the original on 24 September 2015. Retrieved 9 October 2014.
  5. "Exclusive: Agent Tips Osinachi Ohale To Be An Instant Hit At Houston Dash". AllNigeriaSoccer.com. All Nigeria soccer Website. Retrieved 9 October 2014.
  6. "Super Falcons star moves to Växjö DFF in Sweden". Pulse.ng. Pulse.ng. Retrieved 17 September 2019.
  7. "Osinachi Ohale: Super Falcons defender joins CD Tacon from Vaxjo DFF". Goal.com. Goal.com. Retrieved 17 September 2019.
  8. https://www.asroma.com/en/news/2020/7/osinachi-ohale-joins-roma-women
  9. https://www.asroma.com/en/news/2020/7/ohale-impressed-by-spirit-as-she-joins-up-with-new-teammates
  10. "Osinashi Ohale on Goal.com Website". Goal.com. Goal.com Website. Retrieved 9 October 2014.
  11. "IFFHS WOMAN TEAM - CAF - OF THE DECADE 2011-2020". IFFHS. 28 January 2021.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Osinachi Ohale
  • Bayani a Houston Dash
  • Osinachi Ohale