[go: up one dir, main page]

Jump to content

Ikeja Cantonment

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ikeja Cantonment

Ikeja Cantonment wani katafaren sansanin Sojojin Najeriya ne da ke yankin arewacin Legas. Tana nan daga arewaci tsakiyar gari kusa da gundumomin Isolo da Onigbongo.[1]

Ƙisan kiyashi

[gyara sashe | gyara masomin]

A yayin juyin mulki da aka yi a Nijeriya a shekarar 1966 na 28-29 ga Yuli, 1966, Lt. Col. MO Nzefili ya ce an samu rahoton kisan kiyashi a sansanin.[2]

Ta zamo gida ga 9 Brigade na shiyya ta 81 na sojojin Najeriya.

A watan Janairun 2002, an yi amfani da sansanin don adana "bama-bamai masu girman gaske" da dama, da Sauran Bama bamai da ake burnewa.[3] Da yammacin ranar 27 ga watan Janairu, gobara ta tashi a wata kasuwar titi da ke kusa da sansanin, wadda ita ma gidan iyalan sojoji ne. Da misalin karfe 18:00 da alama gobarar ta bazu zuwa babban kantin sayar da kayan yaki na sansanin, lamarin da ya yi sanadin fashewar makamai a Legas a shekarar 2002 .

  1. "Lagos blasts leave 600 dead". BBC. 28 January 2002. Retrieved 9 October 2008.
  2. "Nowa Omoigui. "WITNESSES TO HISTORY: - Lt. Col. M. O. Nzefili (rtd) – Part 2". Retrieved 2020-09-07.
  3. Armoury explosion in Lago, Nigeria". World Health Organization. 2002. Archived from the original on May 2, 2003. Retrieved 9 October 2008.