[go: up one dir, main page]

Jump to content

Kogin Cross River (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kogin Cross River
General information
Tsawo 489 km
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 4°35′N 8°25′E / 4.58°N 8.42°E / 4.58; 8.42
Kasa Najeriya da Kameru
Hydrography (en) Fassara
Tributary (en) Fassara
Watershed area (en) Fassara 54,000 km²
River source (en) Fassara Kameru
River mouth (en) Fassara Tekun Guinea
A Map of Cross River
Kogin Cross River da ke bi ta Kamaru da Najeriya
Kogin Cross River kusa da garin Mamfe, Kamaru

Kogin Cross River (sunan asali: Oyono ) [1] shine babban kogi a kudu maso gabashin Najeriya, kuma daga shi aka samo sunan jihar Cross River. Kogin ya fara ne daga kasar Kamaru, inda ya ake kiranshi da suna kogin Manyu. Ko da yake ba da dadewa ba dangane da ka'idojin ruwayen Afirka, magudanar ruwan yana samun ruwansa ne daga yawan ruwan sama kuma yana kara faɗi sosai a lokacin damuna. Sama da kilomitoci 80 kilometres (50 mi) na ruwan zuwa teku yana bi ta cikin dazuzzuka da dama kuma anan ya samar da delta a kusa da inda ta hade da kogin Calabar, kimanin kilomita 20 kilometres (12 mi) fadi da 50 kilometres (31 mi) ne na tsawo tsakanin garuruwan Oron da ke gabar yamma da Calabar, a gabar gabas, fiye da 30 kilometres (19 mi) daga buɗaɗɗen teku. Kogin delta yana zubewa cikin wani faffadan bakin teku wanda yake rabawa tare da ƴan ƙananan rafuka. Yankin yana da fadin kilomita 24 kilometres (15 mi) daga gabarta na Tekun Atlantika. Gabashin gabar tekun yana cikin makwabciyarta wato kasar Kamaru.

Babban magudanar ruwan na Cross River shine kogin Aloma da ke fitowa daga jihar Benue domin hadewa da Cross River a jihar Cross River. Akwai babban titi da ya hade Jihar Cross River ‘yar uwarta Akwa Ibom. Akwai nisa kimanin kilomitoci 21 (13mi) a tsakanin Oron da Calabar ta hanyar jirgin ruwa da kusan kilomita 200 kilometres (120 mi) ta titi. Al'ummar yankin kogin Cross River na amfani da sufurin ruwa a al'adance kuma Calabar nada tashar ruwa mai dadedden tarihi, a cikin kogin Calabar kimanin kilomita 10 kilometres (6 mi) daga haduwarta da Cross River da kuma kusan kilomita 55 kilometres (34 mi) daga teku. Gadar Itu da ke kan Kogin Cross River tana kan babbar hanyar zuwa Itu daga Calabar kuma an ayyana cewa tana daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Gowon ta samu a lokacin da aka kammala ta a shekarar 1975.

Kogin Cross River ta samar da iyaka tsakanin dazuzzukan tropical moist forest ecoregions guda biyu: Cross-Niger transition forests: wanda ke yammacin kogin tsakanin Cross River da Niger, da kuma <a href="./Cross-Sanaga-Bioko%20coastal%20forests" rel="mw:WikiLink" title="Cross-Sanaga-Bioko coastal forests" class="mw-redirect cx-link" data-linkid="131">Cross-Sanaga-Bioko coastal forests</a>, wadanda ke gabas tsakanin Cross River da kuma kogin Sanaga na Kamaru. Matsakaicin ruwan sama na shekara-shekara ya bambanta daga 1,760 mm a arewacin jihar zuwa 3,100 mm a kudancin (WSSSRP II 2016).

Masu raye-raye a cikin tufafin jihar Cross River

Har wayau ana amfani da sunan Cross River a matsayin sunan wurin shakatawa na ƙasa da wasu dangin kalmomina harsuna .

Yankin Cross River yana da matukar muhimmanci a tarihi, kasancewar sa) kusa da wata kasa ta asali wadda daga cikinta ne mutanen Bantu suka yi hijira zuwa mafi yawan yankin kudu da hamadar Saharar Afirka shekaru 3000-5000 da suka wuce, b) wurin da aka kirkiro rubutun Nsibidi, da kuma c) mazaunin Calabar, daya daga cikin manyan cibiyoyi a lokacin cinikin bayi na Atlantic .

  1. Empty citation (help)

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]

4°35′N 8°25′E / 4.583°N 8.417°E / 4.583; 8.417Page Module:Coordinates/styles.css has no content.4°35′N 8°25′E / 4.583°N 8.417°E / 4.583; 8.417