[go: up one dir, main page]

Jump to content

Gibril Ibrahim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gibril Ibrahim
Minister of Finance and Economy (en) Fassara

9 ga Faburairu, 2021 - 19 ga Janairu, 2022
Rayuwa
Haihuwa Darfur (en) Fassara, 1 ga Janairu, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Sudan
Ƴan uwa
Ahali Khalil Ibrahim (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Khartoum
Meiji University (en) Fassara
Harsuna Larabci
Harshen Japan
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Malami da koyarwa
Imani
Jam'iyar siyasa Ƙungiyar Adalci da Daidaito
Gibril Ibrahim

Dr. Gibril Ibrahim Mohammed (Larabci: جبريل إبراهيم محمد‎), wani lokaci ana rubuta Jibril,) ɗan siyasar Sudan ne. Shi ne shugaban kungiyar Justice and Equality Movement (JEM). An zaɓe shi ne don maye gurɓin dan uwansa, Khalil, a ranar 26 ga watan Janairu, 2012, bayan mutuwar Khalil a wani hari ta sama da SAF ta kai a Arewacin Kordofan a watan Disamba 2011.[1] A yakin Sudan 2023, ya yi kawance da SAF.[2]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ibrahim ne a ranar 1 ga watan Janairun 1955 a garin Al-Tina da ke arewacin Darfur, a wancan lokaci da ƙasar Masar ta yi wa Sudan mulkin mallaka. Mahaifinsa ya rasu yana ɗan shekara 4. Ibrahim ya yi karatun digiri na farko a jami'ar Khartoum, kafin ya bar Sudan yana da shekaru 25.[3]

Ibrahim dai ya samu gurbin karatu a kasar Japan, inda ya shafe shekaru 7, inda ya kammala digirinsa na biyu da kuma digirin digirgir a fannin tattalin arziki, sannan ya zama kwararre a fannin magana da harshen Jafananci. Daga baya Ibrahim ya koma Sudan, kafin ya sake tafiya Dubai a shekara ta 2000 saboda adawa da gwamnati. A Dubai ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan tattalin arziki na JEM na tsawon shekaru 6, kafin ya tafi Burtaniya a shekara ta 2006 don zama Sakataren Harkokin Waje na JEM.[3]

Ibrahim ya taɓa koyarwa a matsayin farfesa a jami'a, kuma yana cikin tawagar JEM ta tattaunawa a tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Abuja da Doha.[4]

Ibrahim ya kasance Ministan Kuɗi daga watan Fabrairu 2021 zuwa Oktoba 2021.[5] An ba shi muƙamin a matsayin wani bangare na yarjejeniyar tallafawa juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 25 ga watan Oktoba 2021.

  1. "Sudan Tribune: Plural news and views on Sudan". Retrieved 19 March 2015.
  2. "Sudan civil war: Darfur's Jem rebels join army fight against RSF". BBC News (in Turanci). 2023-11-17. Retrieved 2023-11-19.
  3. 3.0 3.1 "Meet the leadership: JEM Chairman, Dr. Gibril Ibrahim". Archived from the original on 2 April 2015. Retrieved 19 March 2015.
  4. "BBC News - Sudan: Brother of Darfur rebels' late leader takes over". BBC News. Retrieved 19 March 2015.
  5. "Sudan's new Cabinet sworn in amid protests over dire economy". AP NEWS (in Turanci). 20 April 2021.