Gong Li
Gong Li | |||
---|---|---|---|
1998 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Shenyang (en) , 31 Disamba 1965 (58 shekaru) | ||
ƙasa |
Sin Singapore | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama |
Ooi Hoe Seong (en) (Nuwamba, 1996 - 2010) Jean-Michel Jarre (mul) (2019 - | ||
Ma'aurata | Zhang Yimou (en) | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Central Academy of Drama (en) (1985 - | ||
Harsuna |
Sinanci Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | jarumi da ɗan wasan kwaikwayo | ||
Tsayi | 1.6 m | ||
Muhimman ayyuka |
Red Sorghum (en) Raise the Red Lantern (en) Memoirs of a Geisha (en) Farewell My Concubine (en) The Story of Qiu Ju (en) | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
IMDb | nm0000084 |
Gong Li ( Sinanci : 巩俐; an haife ta a ranar 31 ga watan Disamba, 1965) 'yar fim ce' yar asalin ƙasar Singafo wacce aka haifa a kasar Sin, ana daukarta a matsayin daya daga cikin kyawawan mata a China a yau. Ta yi fice a cikin uku daga cikin Kyaututtuka huɗu na Finafinan duniya mafi kayatarwa da aka yi su da yaren China.
Kuruciya
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Gong Li ne a garin Shenyang, Liaoning, China, ita ce auta a jerin yara biyar din da iyayenta suka haifa. Mahaifinta farfesa ne a fannin tattalin arziki kuma mahaifiyar ta malama ce. Ta girma ne a Jinan, babban birnin Shandong . Ta kasance mai son waƙa da rawa tun tana ƙarama, kuma tana da burin zama mawaƙiya.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]1987–1989: Farawar aikinta
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1987, wani darakta mai suna Zhang Yimou ya fara zabar Gong don taka rawa a cikin wani shirin yakin nuna kin jinin Japan mai suna Red Sorghum, wanda a hukumance ya kaddamar da hadin kansu na tsawon shekaru 15 tare da daraktocin ƙarni na biyar na kasar Sin. Fim din ya lashe Gwarzon Zinare a bikin Fim na Kasa da Kasa karo na 38 a Berlin, ya zama fim din kasar Sin na farko da ya fara samun wannan kyauta. Hakanan ya sami lambar yabo ta Golden Rooster da Kyautar Furanni Dari a matsayin fim Mafi Kyawun Hoto a cikin 1988.