Ayaan Hirsi Ali
Ayaan Hirsi Ali ( an haife ta a ranar 13 ga watan Nuwambar 1969) yar Dutch - Amurka himmar aiki wanda aka haifa a ƙasar Somaliya. An san ta da yin suka game da kaciyar mata a Musulunci. Ita ɗiya ce ga ɗan siyasan Somalia, Xirsi Magan Isse. A shekarar 2005 mujallar Times Magazine ta saka Hirsi a jerin mutane 100 mafiya tasiri a duniya. Xirsi Ali ta zama Ba’amurkiya a shekarar 2013. Ta auri masanin tarihin Burtaniya kuma mai sharhi kan jama'a Niall Ferguson .
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Xirsi Ali a matsayin Ayaan Xirsi Magan a shekarar 1969 a Mogadishu, Somalia. An saka mahaifinta Xirsi Magan Ciise a kurkuku lokacin da Xirsi Ali ke jaririya. an yi mata kaciya lokacin da take 'yar shekara biyar. [1] Gidan dangin Ali sun yi ƙaura zuwa Saudi Arabiya sannan kuma Habasha. A 1980 suka sake komawa Nairobi, Kenya. Xirsi Ali ta yi karatu a wata Makarantar Sakandiren Mata ta Musulmai.
Rayuwa a cikin Netherlands da Amurka
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1992 Xirsi Ali ta koma Netherlands. Tsakanin 1995 da 2001 ta yi aiki a matsayin mai fassara. Ta fara aiki a matsayin mai bincike na Gidauniyar Wiardi Beckman a 2001. A 2002 ta zama mara addini . Ta zama memba a majalisar Dutch a 2003. Xirsi Ali ce ta rubuta wani gajeren fim wanda Theo Van Gogh ya bada umarni mai suna Submission. An sake shi a cikin 2004. Mohammed Bouyeri ya kashe Van Gogh a ranar 2 ga Nuwamba 2004. Ya bar rubutu a jikin Gogh. Bayanin ya kasance barazanar mutuwa ga Xirsi Ali. A cikin 2006 littafin Xirsi Ali na biyu da aka fassara cikin Turanci, The Caged Virgin: An Emancipation Proclamation for Women and Islam, an buga shi.
A cikin 2013 Xirsi Ali ta zama 'ƴar ƙasar Amurka.
A shekarar 2014 Jami'ar Brandeis ta yanke shawarar ba wa Xirsi Ali digirin girmamawa. Sannan ba a ba ta digirin ba saboda wani kamfen.
Ra'ayin Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Xirsi Ali na goyon bayan Isra’ila a rikicin Isra’ila da Falasdinu .
Gidauniyar AHA
[gyara sashe | gyara masomin]A 2007 Xirsi Ali ta fara gidauniyar AHA . Gidauniyar ita ce don 'yancin mata.