Adebisi Akande
Adebisi Akande | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003 ← Theophilus Bamigboye (en) - Olagunsoye Oyinlola → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ila Orangun, 23 ga Janairu, 1939 (85 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
All Progressives Congress Alliance for Democracy (en) |
Abdukareem Adebisi Bamdele Akande ("Bisi Akande"; an haife shi a ranar goma sha shida 16 ga watan Janairu shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da tara 1939) shi ne gwamnan jihar Osun, Nijeriya daga shekara ta (shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara 1999 zuwa shekarar alif dubu biyu da ukku 2003) a matsayin memba na jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), kuma shi ne Shugaban riko na farko na All Progressives Congress.
Farkon rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Cif Adebisi Akande an haife shi a Ila Orangun a ranar goma sha shida 16 ga watan Janairun shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da tara 1939 a yankin da ake kira Osun Central Senatorial a yanzu. An zabe shi ne a kan dandalin Unity Party of Nigeria (UPN). An bayyana Akande a matsayin dan wa ga Cif Bola Ige.
Aikin gwamna
[gyara sashe | gyara masomin]An zaɓi Akande a matsayin gwamnan jihar Osun a watan Afrilun shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) yana takarar jam’iyyar Alliance for Democracy (AD), wacce a baya-bayan nan ta kafa kungiyar siyasa ta kungiyar yarbawa ta Afenifere. Ya gaji Kanar Theophilus Bamigboye, wanda aka nada a matsayin mai kula da mulkin soja na jihar a watan Agustan shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da takwas (1998) wanda kuma ya mika mulki a ranar ashirin da tara 29 ga watan Mayu a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) A ranar talatin da daya 31 ga watan Mayu a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) Akande ya kaddamar da majalisa ta biyu a jihar Osun.
Akande ya sake tsayawa takara a shekarar alif dubu biyu da ukku (2003) amma Prince Olagunsoye Oyinlola na jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) ya kayar da shi.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]https://web.archive.org/web/20110724235004/http://www.alliancefordemocracyusa.org/prelease.htm