Andrianjafy
Sarki Andrianjafy (kafin c. 1770-1787) wanda kuma aka fi sani da Andrianjafinandriamanitra da Andrianjafinjanahary, shi ne sarkin Imerina Avaradrano, yankin arewacin tsaunukan tsakiyar Madagascar tare da babban birninsa a Ambohimanga. Mahaifinsa Andriambelomasina ya ba shi gadon sarautar Avaradrano yayin da yake nada ɗan wansa Ramboasalama don ya bi Andrianjafy a matsayin magaji. Andrianjafy bai amince da wannan doka ba, a maimakon haka ya gwammace dansa ya gaje shi, kuma ya nemi ramuwa a kan 'yan kasar Avaradrano wadanda suka amince da ikon dan uwan nasa.
Andrianjafy | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1770 |
ƙasa | Madagaskar |
Mutuwa | Ilafy (en) , 1787 |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Andriambelomasina |
Sana'a | |
Sana'a | sarki |
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.